IQNA

18:07 - February 07, 2012
Lambar Labari: 2270658

Faddar Tasirin Kiyayya Da Yahudancin Sahyuniya Ya Samo Asali Ne Daga Juyin Iran

Bangaren kasa da kasa, fadadar tasirin kiyayya da yahudancin sahyuniya a duniya musamman a cikin kasashen musulmi da na larabawa ya samo asali ne daga juyin juya halin muslunci da ya gudana a kasar Iran kimanin shekaru talatin da uku da suka gabata.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mataimakin shugaban cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun muslunci Muhammad Reza ya bayyana cewa, ko shakka babu fadadar tasirin kiyayya da yahudancin sahyuniya a duniya musamman a cikin kasashen musulmi da na larabawa ya samo asali ne daga juyin juya halin muslunci da ya gudana a kasar Iran kimanin shekaru talatin da uku da suka gabata da ya ginu kan kiyayya da duk nauin zalunci kan al’ummomin duniya.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
948521



captcha