IQNA

Raya Addinin Muslunci Shi Ne Babbar Manufar Juyin Juuya Halin Muslunci A Iran

14:32 - February 08, 2012
Lambar Labari: 2271210
Bangaren kasa da kasa, shugaban tawagar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon taron makon hadin kai a Iran ya sheda cewa bababr manufar juyin juya halin muslunci a Iran ita ce raya addinin muslunci, kamar yadda aka gani a kasa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nur cewa, shugaban tawagar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon taron makon hadin kai a Iran ya sheda cewa bababr manufar juyin juya halin muslunci a Iran ita ce raya addinin muslunci, kamar yadda aka gani a kasa bayan samun nasarar juyin juya halin.
A bangare guda kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar a daren jiya a wani taron maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Beirut, wanda ya samu halartar dubban mutane da kuma saka bayanin a cikin talabijin kai tsaye.
A cikin jawabin nasa Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa wajibi ne al'umamr musulmi ta zama cikin fadaka, domin kuwa makiya wannan al'umma ba su taba daga kafa ba wajen shirya mata makirci, kuma babban abin da ke gabansu a halin yanzu shi ne kokarin ganin sun rarraba kan musulmi, ta yadda hakan zai ba su dammar yi wa musulmi kwaf daya a lokacin da suka yi rauni tare da shagaltuwa da banbancen da ke tsakaninsu.
Sayyid Nasrullah ya mayar da martini dangane da masu zargin cewa Iran ce take tafiyar da dukaknin lamurran kungiyar, inda ya ce hakika jamhuriyar muslunci tan baiwa kungiyar Hizbullah taimako tun daga lokacin da aka kafa kungiyar a cikin shekara ta 1982 har zuwa inda yau take, amma kungiyar ce da kanta take fayyace abin da take yi, da kuma wanda za ta yi.
949158

captcha