IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Kara Jaddada Matsayinta Na Riko Da Gwagwarmaya

18:36 - February 09, 2012
Lambar Labari: 2271842
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hizbullah a kasar Lebanon ta jaddada matsayinta na yin riko da tafarkin gwagwarmaya domin taka wa haramtacciyar kasar Isra’la birki kan shishiginta a kan kasar Lebanon da kuma kwao sauran yankunan da a halin yanzu suke karkashin haramtacciyar gwamnatin yahudawan.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, wakilin kungiyar hizbullah a kasar Lebanon ya jaddada matsayinta na yin riko da tafarkin gwagwarmaya domin taka wa haramtacciyar kasar Isra’la birki kan shishiginta a kan kasar Lebanon da kuma kwao sauran yankunan da a halin yanzu suke karkashin haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Babban magatakaradan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya ce shugaban kungiyar Larabawa ya sanar da shi cewa kungiyar a shirye ta ke ta sake tura tawagar masu sa ido a kasar Siriya.
A jiya Laraba Ban Ki-Moon ya ce shugaban kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Nabil al-Arabi ya sheda masa a zantawa da suka yi ta wayar tarho a ranar Talata cewa da akwai shirin sake aikewa da tawagar masu sa ido zuwa kasar Siriya.
Al-Arabi ya kuma bukaci sa hannun MDD don aikin ya kasance na hadin guiwa tsakanin MDD da kungiyar Larabawan, tare kuma da tura jakada na musamman shi ma na hadin guiwa.
Ban Ki-Moon ya bayyana takaicinsa kan rashin cimma daidaiton baki a kwamitin tsaro dangane da fitar da kuduri kan kasar Siriya amma kasar Rasha da ta hau kujerar na-ki ta ce ba zata bada dama kasashen Yamma a sake yin amfani da kudurin MDD don daukar matakan soji kan wata kasa kamar yanda suka yi a kasar Libya ba.
949962

captcha