Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun muslunci ta kasasashen musulmi ISESCO ta jaddada cewa samun kyakyawar fahimta a tsakanin mazhabobin addinin muslunci shi ne bababn abin da zai had akan al’ummar musulmi a wannan zamani. Ana sa ran babban sakataren kungiyar zai halarci zaman taron kusanto da fahimtar juna da hadin kan al’ummar musulmi da ke gudana a birnin Tehran.
A jiya laraba ne aka bude babban zaman taron makon hadin kai na kasa da kasa karo na ashirin da biyar a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, zaman da ya samu halattar manyan baki daga sassa daban daban na duniya.
Zaman babban taron makon hadin kai na kasa da kasa karo na ashirin da biyar a wannan shekara ya samu halattar manyan jami'an gwamnatocin kasashe, manyan malaman addinin Musulunci da kuma masana da manazarta da suka fito daga kasashe 57 na duniya, kuma mabiya mazhabobin Musulunci daban daban.
Babban sakataren cibiyar kasa da kasa domin samar da hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci Ayatullahi Sheikh Muhammad Ali Taskhiri ne ya bude zaman taron, inda a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Hakika albarkacin fadakar Musulunci an samu haihuwar sabon yankin gabas ta tsakiya ta hanyar da ta yi hannun riga da bakar manufar siyasar gwamnatin Amurka.
Sheikh Maulawi Muhammad Is'hak Madani Shugaban Majalisar Kolin Cibiyar kasa da kasa domin samar da hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci a nashi jawabin ya furta cewa: Lalle fadakar Musulunci da ta kunno kai a wannan zamani ta samo asali ne sakamakon zubar da jinin dubban shahidai a kasashen musulmi, kuma wajibi ne a kan al'umma sun jure duk wata wahala, matsin lamba da takunkumi domin cimma manufar wannan yunkuri na fadakar Musulunci a kasashensu.
949947