IQNA

An Yi Taron Tunawa Da Juyin Juya Halin Muslunci Na Iran A Birtaniya

19:57 - February 13, 2012
Lambar Labari: 2273582
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro na tunawa da juyin juya halin muslunci a kasar Iran wanda aka yi birnin London fadar mulkin kasar tare da halartar malaman addinin muslunci da kuma wadanda suka karanta harshen farisanci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa nayanr gizo na ic-el cewa, an gudanar da wani taro na tunawa da juyin juya halin muslunci a kasar Iran wanda aka yi birnin London fadar mulkin kasar tare da halartar malaman addinin muslunci da kuma wadanda suka karanta harshen farisanci a kasar da ma wasu daga cikin wakilan cibiyoyin addini.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labarin kuma limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya.
Har ila yau limamin ya ce wasu daga cikin dalilan matsa kaimi da kasashen yamma musamman ma Amurka ke yi a kan Iran, sun hada da yadda al'ummomin kasashen wannan yanki suka juya mata baya, saboda haka suke zargin Iran da hannu a shirya irin wannan bore da ke gudana. To sai dai Ayatullah Imami-Kasheni ya ce shirun da kasashen duniya suka yi dangane da wannan ta'addanci da ake aikatawa a kan Iran, wata alama ce da ke nuna da irin goyon bayan da masu wannan shiru ke bai wa ayyukan ta'addanci a duniya.
951579


captcha