IQNA

19:57 - February 13, 2012
Lambar Labari: 2273584

Mahukuntan kasar Bahrain Na Kai Farmaki Kan Gidajen Jagororin ‘Yan Adawa

Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin jagororin masu adawa da salon mulkin kama karya na kasar Bahrain ya bayyana cewa jami’an tsaron kasar tare da ‘yan bangar masarautar kasar suna ci gab ada kai farmaki kan gidajen wadanda suke jagorantar zanga-zangar neman sauyi a fadin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na tashar Al-alam cewa, daya daga cikin jagororin masu adawa da salon mulkin kama karya na kasar Bahrain ya bayyana cewa jami’an tsaron kasar tare da ‘yan bangar masarautar kasar suna ci gab ada kai farmaki kan gidajen wadanda suke jagorantar zanga-zangar neman sauyi a fadin kasar da hakan ya hada birnin Manama, da ma wasu sauran yankuna.
Wani labarin kuma ya ce limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya.
Har ila yau limamin ya ce wasu daga cikin dalilan matsa kaimi da kasashen yamma musamman ma Amurka ke yi a kan Iran, sun hada da yadda al'ummomin kasashen wannan yanki suka juya mata baya, saboda haka suke zargin Iran da hannu a shirya irin wannan bore da ke gudana.

951577
captcha