Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wani masanin harkokin siyasar gabas ta tsakiya yana fadar cewa saboda tsabar fadin gaskiya ba tare da wasu kwane-kwane ba hakan ya sanya yahudawan sahyniya da dama sun fi gasgata zancen sayyid Hassan Nasrullah shugabanninsu na siyasa ko na soji, kamar su kansu yahudawan suka tabbatar da hjakan a lokacin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Lebanon.
Jam’iyyar Likud mai tsananin tsatsauran ra’yi kan akidar sahyuniyanci ta kudiri aniyar kaddamar da wani farmaki kan masallacin Qods mai alfarma da nufin rushe wurare masu tsarki a wurin muslumi da kuma mabiya addinin kirista ta hanyar yin amfani da ‘yan bangar wannan jamiyya.
Bangare guda kuma shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya. 953084