Bangaren kasa da kasa; a karo na ashiri za a gudanar da taron karawa juna sani kan ranar aihuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka a ranar shidda ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shmasiya da kuma aka bawa wannan taron taken raya soyayya da kauna ga ma'aikin Allah Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a garin Misisaga na lardin Antarivo na kasar Kanada.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na ashiri za a gudanar da taron karawa juna sani kan ranar aihuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka a ranar shidda ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shmasiya da kuma aka bawa wannan taron taken raya soyayya da kauna ga ma'aikin Allah Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a garin Misisaga na lardin Antarivo na kasar Kanada.Da misalin karfe biyu zuwa karfe tara na daren agogon kasar a cibiyar fasaha da al'adu ta garin ne za a gudanar . Wannan taron karawa juna sani kan muhimmancin soyayya da nuna kauna ga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa zai taro malamai dam asana da za su fito daga kasashe daban daban kamar Pakistan ,Britaniya,Amerika da kuma Kanada mai masabkin baki.
953763