IQNA

17:48 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275343
Bangaren siyasa: ministan harkokin wajan kasar kasar Iran ya aike da sakonni daban daban ga shugabannin hukumomi da cibiyoyi na yankin gabas ta tsakiya da kuma na kasa da kasa kan halin takaici da takurawa da al'ummar kasar Bahrain ke ciki inda gwamnatin wannan kasa da karfi day a wuce mizani da hankali ke neman murkushe boren neman kawo sauyi da canji a kasar da kuma yadda wasu kasashen waje ke yin shiga shigula a cikin lamarin fararen hula a kasar.Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ministan harkokin wajan kasar kasar Iran ya aike da sakonni daban daban ga shugabannin hukumomi da cibiyoyi na yankin gabas ta tsakiya da kuma na kasa da kasa kan halin takaici da takurawa da al'ummar kasar Bahrain ke ciki inda gwamnatin wannan kasa da karfi day a wuce mizani da hankali ke neman murkushe boren neman kawo sauyi da canji a kasar da kuma yadda wasu kasashen waje ke yin shiga shigula a cikin lamarin fararen hula a kasar. An jiyo daga ofishin watsa labarai da bayanai na ma'aikatar harkokin wajan kasar Iran cewa bias la'akari da mummunan hali da al'ummar Bahrain ke ciki a yan kwanakin nan da kuma yadda gwamnatoci na yankin da kuma na sauran kasashen duniya da kuma uwa uba hukumomi da cibiyoyi na yankin da na kasa da kasa suka yi gum da bakinsu ya tilastawa ministan harkokin wajan kasar Iran aikewa da wasu sakonni na tayar das u daga barci kan halin da al'ummar kasar Bahrain da ke neman kawo sauyi da canji a harkokin kasar su ke ciki da kuma ke bukatar hukumomi da cibiyoyi na yankin da na kasa da kasa sun fadaka da maida hankali da halin da suke ciki na kasha su da takura masu da gwamnatin sarkin Bahrain ke yi a kokarinta na ganin ta kawo karshen wannan yunkuri na al'ummar kasar na neman kawo sauyi ta karfin soja tare da taimakon kasar Saudiya.
953772

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: