IQNA

21:20 - February 18, 2012
Lambar Labari: 2276416

Ana Shirin Gudanar Da Wani Zaman Taro Mai Taken Kur'ani A Duniyar Yau

Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Amurka sun sheda cewa ana shirin gudanar da wani zaman taro a birnin Princeton na jahar New Gercy da ke kasar Amurka mai taken alkur'ani mai tsarki a duniyarmu ta yau.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa ta yanar gizo na winst cewa, a halin da ake ciki rahotanni daga kasar Amurka sun sheda cewa ana shirin gudanar da wani zaman taro a birnin Princeton na jahar New Gercy da ke kasar Amurka mai taken alkur'ani mai tsarki a duniyarmu ta yau tare da bayyana matsayin musulmi a kan abubuwa da dama da suke faruwa a duniya da ake danganta su da addinin muslunci domin bata sunasa.

Sa'anan kuma al'umma ne za su zabi shugaban kasa da kansu, maimakon zaben shi a majlaisar dokoki, kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar kafa jam'iyun siyasa ba tare da wani haddi ba, kuma babu wani fifiko ga wata jam'iyya a kan wata. Haka nan kuma shugaban kasa dole addininsa ya zama muslunci, amma bisa sharadin zai girmama sauran addinai da ke kasar naki daya ba tare da nuna banbanci a tsakanin mabiyansu ba.

Wannan zaman taro na da matukar muhimamnci ta fuskoki da dama, da suka hada da bayyana muslunci kamar yadda yake sabanin yadda ake bayyana ma duniya shi da nufin bata shi, musamman ma a cikin kasashen turai.

954227

captcha