Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai kwashe tsawon mako guda ana gudanar da shi a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon mai taken makon Imam Hussain (AS) tare da halartar masana da kuma malaman addini daga cikin ta Lebanon da kuma kasar Iraki, da hakan ya hada da birnin Karbala mai alfarma.
A wani bangare na sabon kundin tsarin tsarin mulkin kasar, ya bayar da 'yancin bude kafofin sadarwa masu cin gishin kansu, da kuma damar gudanar da taruka na siyasa da 'yancin bayyana ra'ayi, haka nan kuma bangaren shari'ar kasar zai kasance mai zaman kansa, tare da shiga kafar wando daya da duk wanda ya aikata laifi komai matsayinsa, da kuma yakar cin hanci da rashawa a dukaknin bangarorin gwamnati, da ma tsakanin jamaa'a, kamar yadda hukumar zabe za ta kasance mai cikakken iko da cin gishin kanta, ba tare da karbar umurni daga wani bangare da ke cikin siyasar kasar ba, da ma dai sauran batutuwa da dama da sabon kundin tsarin mulkin ya kunsa.
Masu bin digging lamurran da ke kai da komowa sun amannar cewa, idan al'ummar kasar Syria suka amince da wannan sabon kundin tsarin mulki, kuma aka samu damar aiwatar da dukaknin abin da ya kunsa, to hakan zai mayar da kasar abin koyi ta fuskacin demokradiyya ga sauran kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya, wadanda akasarinsu ba su taba sanin wani abu demokradiyya a cikin kasashensu ba, inda sarki ne wuka da nama a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa a kasa. 954858