Bangaren kasa da kasa; kasar Chana ta guduri aniyar gina gurin ajiya da ganin kur'ani masu tsarki da suka jima kuma wannan wani mataki ne na ajiyar kayan tarihi na musulmi da wani abubuwa na tarihin musulmi a kasar da kuma zai zama mafi girma a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarkin a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kasar Chana ta guduri aniyar gina gurin ajiya da ganin kur'ani masu tsarki da suka jima kuma wannan wani mataki ne na ajiyar kayan tarihi na musulmi da wani abubuwa na tarihin musulmi a kasar da kuma zai zama mafi girma a yankin.Kimanin kudinYu'an na kasar Chana miliyon hudu aka ware domin gina wannan cibiya a kan fili murabba'I dari takwas kuma a shekara mai kamawa ne za a fara wannan aiki na tarihi mai tarihi da alfano ga musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba a ciki da wajan kasar ta Chana kuma a kasa da shekara daya ne ake hassashen kammala wannan aiki mai muhimmanci.
955121