Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Almalifi marubuci dan salafiya dan kasar Koweiti da ya muzanta ingantattun bayanai masu daraja da suka shafi Imam Mahdi (AJ) kotu ta zartar masa da hukumcin zama a gidan yari. A ranar talatin ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kotun kasar Koweiti ta fitar da bayanin cewa: Muhammad Almalifi zai ci gaba da zama a gidan maza da ci gaba da tsare shi har zuwa ranar kwanaki ashirin da daya a nan gaba wato har zuwa ranar ashirin da daya ga watan Isfand kafin ta kammala bincike da nazari kansa.Kotun ta bayyana cewa; Muhammad Almalifi ana zarginsa da cin fuska da mazhabar Shi'a kuma babban kokarin makirci ne na rugua hadin kan kasa kuma wani kokari ne natada fitina kuma za a ci gaba da tsare shi. Har ila yau a jiya ne aka fara sauraren masu masu shigar da karasa.
956732