Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi Allah wadai da yadda a ke samin karuwar gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a yankin yammacin kogin jodan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi. A cikin wata sanarwa da gidan talbijin na almanar ya watsa kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ta yi kaukausar suka kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma take takenta na takalar fada da neman tada fitina ta hanyar mamaye yankunan Palsdinu da takurawa Palasdinawa a yankuna daban daban na Palsdinu musamman yankin yammacin kogin jodan da ci gaba da fadada siyasarta ta gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna .A baya bayan nan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi alkawalin gina wasu sabbin gidaje na matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a a wani kauye da suka bawa sunan Shilo da ke kusa da Ramalla da Nablus da wannan mataki ke nuni karara da take take da takalar fada da ci gaba da siyasar mamaye ta gwamnatin wuce gonad a iri ta haramtacciyar kasar Isra'ila.
959244