Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shfain sadarwa na yanar gizo na tashar Al-tawafuq cewa, karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
Wannan dai shi ne karon farko da za a fitar da wata jarida ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa a kasar ta Masar.
960003