Kamfannin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani ami girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ma'aikatar harkokin wajan jamhuriyar musulunci ta Iran ta fitar da wani bayani na yin Allah wadai da yadad wasu sojojin mamaye na Amerika da na kungiyar tsaro ta Nato a kasar Afganistan suka ci mutuncin kur'ani mai girma . a cikin wannan bayani da ma'aikatar harkokin wajan ta jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; a wani sabon karo sojojin mamaye na Amerika da na kungiyar tsaro ta Nato a wannan kasar sun sake take hakkin dan adam da kaita hurumin kasa da kasa inda sojojin mamaye na Amerika suka kona kur'ani mai girma a sansanin sojinsu da ke birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan. Wannan cin fuska musulmi ba za su taba kalewa ba kuma musulmin duniya sama da biliyan daya da rabi na yin Allah wadai da tofin Allah tsine da kiran a hukumta duk wani sojin amerika da ke kasar Afganistan da ked a hannu a wannan mummunan aiki na takalar fada da neman haddasa fitina a kjasar musulmi kuma wannan bas hi ne karon farko bad a ake samin irin wannan danyan aiki.
961100