Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’yi ta kasar Kuwait cewa, cibiyar addinin muslunci ta kasar ta Wa zakkir ta yi Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da sojojin ammayar Amurka suka yi a kasar Afghanistana cikin makonni biyu da suka gabata ba tare da wata kasar larabawa ta fito a hukumance ta yi Allawadai da hakan ba.
Jakadan kasar Saudiyya a kasar Masar ya mayar da martani kan zargin da ake yi mahukuntan kasarsa da baiwa tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Tunisia mafaka, da kuma aikewa da sojoji zuwa zu Bahrain domin murkushe masu zanga-zangar lumana, da yin shigar-shigula a cikin harkokin Yemen.
Jakadan na Saudiyya a Masar Ahmad Abdulaziz Qattan ya mayar da martanin ne kan 'yan siyasa na kasashen Masar da Tunisia da ma kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen larabawa, wadanda suke zargin kasarsa da yin harshen damo kan abubuwan da suke faruwa a kasashen larabawa, inda ya ce Zainul abidin tsohon shugaban Tunisia ya bukaci mafaka ne daga Saudiyya, shi ya sanya ta ba shi mafaka, kuma 'yan siyasar Masar da suke sukar lamirin Saudiyya kan hakan, ya ce ai kasar Masar ce ta baiwa tsohon sarki Shah na kasar Iran mafaka, duk kuwa zaluncin da ya yi wa al'ummar Iran a lokacin mulkinsa.
Dangane da kare masarautar Bahrain da murkushe masu zanga-zangar lumana a kasar da sojojin Saudiyya suke yi, da shigar-shigular da ta ke a cikin harkokin Yemen kuwa, jakadan na Saudiyya a Masar ya yi ta inda-inda, inda ya gaza kawo kwararn dalilai na yin hakan.
964943