Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na paktribune cewa, 'yan majalisar dajjitai a kasar Pakistan sun yi kira da a dauki kwararn matakai kan masu keta alfarmar kur'ani a ko'ina ne cikin fadin duniya domin hakan ne kawai zai kawo karshen abin da ake yi an tsokanar mabiya addinin muslunci ta hanayar wulakanta abubuwan da suke girmamawa kamar yadda muka gani a cikin kawanakin na a kasar Afghanistan, inda sojojin Amurka suka kone kur'ani mai tsarki.
A wani bangare kuma a ci gaba da keta alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan sahyuniya suke yi a cikin yankunan palastinu da suka hada da masallacin Qods, malaman addinin Musulunci sun yi gargadi kan irin hatsarin da birnin Qudus da Masallacin Aksah suke fuskanta.
Babban limamin masallacin Aksa Sheikh Akramah Sabari a yau alhamis ya gargadi gwamnan birnin Qudus kan manufar yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida na neman kutsawa cikin masallacin Aksah bayan da suka fara zuwa wani yankin filin da ke cikin masallacin. Sheikh Sabari ya bayyana cewa; filayen da suke kewayen masallacin Aksah suna daga cikin harabar masallacin Aksah ne don haka dole ne mahukuntan haramtacciyar kasar Isra'ila su dauki matakin shawo kan wannan wuce gona da iri domin tsoron abin da zai biyo baya.
A nashi bangaren Sheikh Yusuf Adi'is shugaban kotun kolin shari'a ta yankin Palasdinu ya bayyana cewa; lalle masallacin Aksah yana fuskantar hatsari mai tsanani, saboda a halin yanzu 'yan majalisun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida suna shirin ganin sun rusa masallacin na Aksah domin maye gurbinsa da wajen bautansu da suke da'awar kasantuwarsa a wannan mahallin.
967522