Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin malaman addinin muslunci a Lebanon Sheikh Muhammad Namir ya bayyana cewa wasu daga cikin kasahen duniya hard a wadanda suke raya kare hakkin bil adama da kuma kasashen musulmi da na larabawa sun yi gum da bakinsu kanta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila take tafkawa kan alaummar palastinu wanda hakan ke kara karfafa gwiawar gwamnatin yahudawan wajen ci gabada ta'asarsu.
Wata majiyar tsaron kasar Masar ta bayyana cewar an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Palastinawa da HKI don kawo karshen hare-haren ta'addancin da sojojin HKI suka kaddamar a kan al'ummar Gaza da ya yi sanadiyyar shahadar Palastinawa 26 da raunana wasu da dama.
Majiyar tace kasar Masar din ne ta cimma wannan yarjejeniyar tsakanin bangarorin biyu a wata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin bangarorin biyu. Majiyar ta ce kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan sun amince da wannan yarjejeniyar. Wata majiyar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihad Islami ta bayyana cewar ta amince da wannan yarjejeniyar ne amma da sharadin cewa HKI za ta dakatar da wadannan ayyukan ta'addanci.
Cimma yarjejeniyar dai ta zo ne a daidai lokacin da wasu jaridun HKI suke bayyana cewar ya zuwa yanzu dai dakarun gwagwarmayar Palastinawan sun harbe sama da makamai masu linzami 200 cikin HKI lamarin da ya sanya yahudawan cikin halin damuwa da zaman dardar duk kuwa da garkuwar kakkabo irin wadannan makamai da suka kafa.
Wasu majiyoyin HKIn sun yi amanna da cewa daya daga cikin dalilan da suka sanya HKIn amincewa da tsagaita wutan yana da alaka da irin ci gaba da hare-haren da dakarun gwagwarmayar suke kai wa matsugunan yahudawa da makamai masu linzamin.
971193