Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, A jawabin da ya gabatar wa al'ummar 'yan sa'oin da suka gaba, wanda kuma a watsa kai tsaye a dukaknin gidajen talabijin din kasar, jagoran ya bayyana wannan shekara da cewa shekara ce ta yin aiki tukuru domin kara habbaka tattalin arzikin kasar, tare da kuma kara zage dantse domin dogaro da kai, bisa la'akari da karuwar matsin lamabar kasashen yammacin turai a kan jamhuriyar muslunci ta Iran.
A bangare guda jagoran ya kirayi dukaknin al'ummar kasar da su kara zam a cikin fadaka dangane da irin makircin da makiya suke kitsa wa kasar, da nufin durkusar da ita, tare da fuskantar kalubalen da ke gabansu na ciyar da kasar su gaba, da kuma kare martabar addininsu a cikin kowane irin yanayi.
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid ali Khamneni ya bayyana cewa, Iran ba ta mallakar makaman nukiliya, kuma ba ta da niyyar mallakarsu, amma kuma za ta ci gaba da shirinta na makamashin nukiliya domin ayyukanta na fararen hula.
Jagoran ya bayyan ahakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a yammacin yau a gaban dubabn daruruwan mutanen da suka taru a hubbaren Imam Rida (AS) da ke birbnin Mashhad, inda ya jadadda cewa, makiya Iran sun fi kowa sanin cewa shirinta na makamshin nukiliy aba na kera makaman kare dangi ba ne, ammakuma saboda manufofi na siyasa suna ci gaba da matsin lamba kan Iran da nufin durkusar da ita, ko kuma tilasta bin bakaken manufofinsu, abin da ya ce da yardar Allah ba zai tab afaruwa ba.
A bangare guda kuma jagoran ya kirayi dukaknin al’ummar kasar Iran da su kara zage dantse wajen ganin sun ciyar da kasarsu gaba, tare da baiwa maras da kunya, kuma su kasance masu sadaukantar da kai domin kar martabar addinin muslunci a kowane lokaci.
974408