Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran mahmud Ahmadijad ya bayyana cewa, ranar idin nourooz rana ce mai matkar muhimmanci ga dukaknin mutanen duniya masu son rayuwa cikin 'yanci da kuma son zaman lafiya a tsakanin 'yan adam abaki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin jawabin da ya gabatar na taya murna ga mutanen jamhuriyar Musulunci ta Iran shugaban kasar mahmud Ahmadijad ya bayyana cewa, ranar idin nourooz rana ce mai matkar muhimmanci ga dukaknin mutanen duniya masu son rayuwa cikin 'yanci da kuma son zaman lafiya a tsakanin 'yan adam abaki daya tare da neman sulhu tsakaninsu da sauran al'ummomi.
Shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya yi alkawarin ganin gwamnatinsa ta kara matsa kaimi wajen shimfida adalci da gudanar da hidima ga al'umma a wannan sabuwar shekara ta Shamsiyya da aka shiga a yau talata.
A sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ta 1391 Shamsiyya; Shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana cewa: Shekarar da ta gabata tana cike da daukaka, farin ciki da gagarumar nasara da al'ummar Iran da ma sauran al'ummomi 'yantattu na duniya suka samu a bangarori da dama na rayuwa, kamar yadda shekarar da shude dauke da abubuwan bakin ciki da na takaici.
Ahmadi Najad ya kara da cewa: Shekara ta 1390 da ta gabata al'ummar Iran sun samu gagarumar nasara da ci gaba a fage da dama musamman bangaren habakar tattalin arziki, ilimi, masana'antu da siyasa, amma da yardan Allah a wannan sabuwar shekara; kasar Iran zata matsa kaimi domin ganin ta ninka ci gaban da ta samu a baya.
974394