IQNA

22:21 - March 29, 2012
Lambar Labari: 2295721

Masautar Bahrain Ta Nuna Rashin Jin da Kan kalaman Shugaban Majalisar Lebanon

Bangaren kasa da kasa, wasu kalamai da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa, wasu kalamai da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar wadanda suke samun goyon baya daga sauran kawayensu ‘yan kama karya na tekun fasha.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Bahrain ta nuna maitar a fili tun daga lokacin da al’ummar kasar suka fara boren neman sauyi, da nufin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar kasar wadanda suke fuskantar zalunci da danniya tswon shekaru na tarihin kasar, amma abin da yafi komai ban mamaki shi ne yadda kasashen larabawa suka yi gum da bakunansu kan ta’asar da gwamnatin ta Bahrain take tafakawa.
Kalaman da Nabih Birri shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar wadanda suke samun goyon baya daga sauran kawayensu ‘yan kama karya na tekun fasha da suka shahara da kama karya a tarinsu da masarautunsu.
975971
captcha