Bangaren kasa da kasa, wakilin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait Ayatollah Muhammad Baqir Almihri ya kirayi malamin wahabiyawan Saudiyya zuwa ga mneman uzuri ga dukaknin musulmin duniya kan cin zarafin da ya yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka.
i
Kamfanin dillancin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an tashar talabijin din Al-alam da ke watsa shirye-shiryensa kai tsaye kan tauraron dan adam daga kasar Iran cewa, wakilin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait Ayatollah Muhammad Baqir Almihri ya kirayi malamin wahabiyawan Saudiyya zuwa ga mneman uzuri ga dukaknin musulmin duniya kan cin zarafin da ya yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka, tare da jingina karya ga wannan manzon mai tsarki.
Mutumin wanda ake kira malami a kasar Saudiyya wanda ya shahara da yin izgili da addinin muslunci da manzon Allah da iyalan gidansa tsaraka mai suna Uraifi, ya raya cewa gjiya ba najasa ba ce, domin kuwa a karyarsa kafin haramta giya wasu daga cikin sahabbai suna baiwa manzon Allah giya kyauta, shi kuma yana zubar da ita ko kuma shi ma ya baiwa wasu kyauta.
Wannan cin zarafi ga addini ne ya sanya wakilin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait Ayatollah Muhammad Baqir Almihri ya kirayi wannan mutum bahawabiyan Saudiyya zuwa ga mneman uzuri ga dukaknin musulmin duniya kan cin zarafin da ya yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka ba tare da wani bata lokaci ba.
976352