IQNA

Rayuwar Musulunci Ta Fara Dawowa A Tsakanin Al’ummar Tunisia

16:13 - April 02, 2012
Lambar Labari: 2296618
Bangaren kasa da kasa, rayuwar muslunci ta fara dawowa atsakanin al’ummar kasar Tunisia ta fuskokin zamantakewa da siyasa kamar yadda za a iya sheda hakan daga yanayin dabiu da halayen jama’a tun bayan samun nasarar juyin juya halin da ya kai ga kawo karshen tsohuwar gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo cewa, jagoran kungiyar nahda a Tunisia Rasid Ganushi ya sheda cewa, a halin yanzu rayuwar muslunci ta fara dawowa atsakanin al’ummar kasar Tunisia ta fuskokin zamantakewa da siyasa kamar yadda za a iya sheda hakan daga yanayin dabiu da halayen jama’a tun bayan samun nasarar juyin juya halin da ya kai ga kawo karshen tsohuwar gwamnati ta tsohon shugaban mulki kama karya na kasar.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Tunisiya ta kara waadin dokar-ta-baci da ake aiki da ita a kasar zuwa karshen wannan wata na Apirilu, kamar yanda wata sanarwar da aka fitar a daren jiya take bayyanawa, kakakin shugaban kasa ya bayyana cewa shugaba Moncef Marzouki ya ba da izinin kara wata guda ne na aiki da dokar-ta-bacin bayan da ya yi shawarwari da shugaban majalisar girka kundin tsarin mulki Mustapha Ben Jaafar da kuma Piraminista Hamadi Jebali.

Sanarwar gwamnatin ta ce dalilan da suka sa aka kara waadin wannan doka su ne barazana iri iri da zasu iya janyo tashe tashen hankali a kasar, wani shaharren dan jarida mai sharhin siyasa na kasar Tunisiya Salahuddin Jorchi ya ce da ma can ana tsammanin gwamnati zata dauki wannan mataki domin har yanzu akwai zaman dar dar a tsakanin alumma duk da cewa an sami kyautatuwar yanayin tsaro.
977053

captcha