IQNA

23:42 - April 08, 2012
Lambar Labari: 2300433

Al’ummar Kasar Syria Ba Su Amince Da Shigar Shigular Kasashen Ketare Cikin Kasarsu Ba

Bnagaren kasa da kasa, al’ummar kasar Syria sun fiito kanmamnyan titinan ksar domin nuna rashin amincewarsu da shigar shigular da wasu kasashen suke yi a cikin harkokin kasar da nufin wargaza duk wani shirin zaman lafiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, al’ummar kasar Syria sun fiito kanmamnyan titinan ksar domin nuna rashin amincewarsu da shigar shigular da wasu kasashen suke yi a cikin harkokin kasar da nufin wargaza duk wani shirin zaman lafiya da tsohon sakataren majalisar dinkin duniya ke jagoranta.
A bangare guda kuma wani bayanin ya ce gwamnatin Syria ta aike da wasu wasiku biyu zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya da kuma shugaban kwamitin tsaron majalisar, dangane da karuwar ayyukan ta'addanci bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
A cikin wasikun biyu, gwamnatin Syria ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta safke nauyin da ya rataya a kanta, wajen matsa lamba kan gwamnatocin da suke taimaka ma ayyukan ta'addanci a cikin kasar Syria, ta hanyar baiwa 'yan bindiga makamai da makudan kudade, domin kuwa a cewar bayanin, idan har gwamnatin Syria za ta amince da wannan yarjejeniya da kuma yin aiki da ita, babu dalilin da zai sanya a bar daya bangaren rikicin yana cin karensa babu babbaka.
Bayanin ya ce tawagogi na masu sanya ido na kasashen larabnawa da majalisar dinkin duniya sun gane wa idanunsu hakikanin abin da ke faruwa a kasar, saboda haka kawo karshen tashin hankali a kasar ya doru ne kan dakatar da kasashen masu taimaka ma ayyukan ta'addanci, musamman ma na larabawa daga cikinsu, wadanda suka sanar da hakan a hukumance.
980244

captcha