IQNA

Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Kyamar Musulmi

17:52 - April 10, 2012
Lambar Labari: 2302061
Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Amurka sun gudanar da wata zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wani malamin addinin kirista ya yi da nufin tsokanan musulmin kasar da ma na duniya baki daya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, mutanen kasar Amurka sun gudanar da wata zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wani malamin addinin kirista ya yi da nufin tsokanan musulmin kasar da ma na duniya baki daya ta hanyar nuna hotunan batunci ga addini.

Kasashen Amurka da kuma Afghanistan sun sanya hannu a kan yarjejeniya mai fayyace yadda za a rika gudanar da sintiri ko kuma kai hare-hare a kan wadanda Amurkar ke zargi da cewa 'yan ta'adda ne a cikin kasar ta Afghanistan, A wani biki da aka gudanar a jiya lahadi a birnin Kabul, ministan tsaron Afghanistan Abdul Rahim Wardak da kuma babban kwamandan sojan Amurka da ke mamaye da kasar Janar John Allen sun sanya hannu a kan yarjejeniya mai cewa daga yanzu wasu sojan kundunbala 'yan asalin Afghanistan da Amurkar ta horas ne za su rika gudanar da wannan aiki, tare da ba su damar yin kutse a cikin gidajen mutanen da ake zargin cewa 'yan ta'adda ne, sabanin yadda a can baya Amurkar ke yin gaban kanta wajen kai irin wadannan hare-hare.

Har ila yau yarjejeniyar ta ce a nan gaba dole ne Amurka ta shawarci rundunar sojan ta Afghanistan da kuma hukumar leken asiri ta kasar kafin kai wani farmaki ko kuma samame a cikin kasar, wanda hakan zai rage yawan sabanin da ake samu tsakanin bangarori biyu. Sau da dama dai Amurka na amfani da jiragen sama maras matuki domin kai farmaki tare da kashe dimbin jama'a a kasar ta Afghanistan sannan kuma ta fito ta ce hakan ya faru ne a kan kuskure.

981486
captcha