IQNA

Za A Gudanar da gagarumar Zanga-Zanga A fadin kasar saudiyya A ranar juma’a

22:09 - April 11, 2012
Lambar Labari: 2303059
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin kasar Saudiyya da nufin tabbatar wa duniya cewa yunkurin da mutanen kasar suke na neman ‘yanci na nan daram duk kuwa da kisa da dauri da mahukuntan wahabiyawan kasar suke yi a kansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabi press cewa, ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin kasar Saudiyya da nufin tabbatar wa duniya cewa yunkurin da mutanen kasar suke na neman ‘yanci na nan daram duk kuwa da kisa da dauri da mahukuntan wahabiyawan kasar suke yi a kansu.
Tun a cikin shekarar da ta gabata ce al’ummar kasar Saudiyya take gudanar da zanga-zangar la’antar gidan Ali-saud masu mulki tsawon shekaru sama da dari daya, wadanda suka shahara da danniya da murkushe mutane farren hula da karfin soji da taimakon turawa, amma duk da haka wannan bai hana mutane ci gaba da yin borensu ba domin neman hakkokinsu.
Ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin kasar Saudiyya da nufin tabbatar wa duniya cewa yunkurin da mutanen kasar suke na neman ‘yanci na nan daram duk kuwa da kisa da dauri da mahukuntan wahabiyawan kasar suke yi a kansu, amma daio za su gaba da neman hakkokinsu da aka haramta musu.
982449


captcha