Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gwamnatin kasar Azarbaijan ta kafa dokar hana kafa jam’iyya mai taken addini a yunkurin da gwamnatin kasar take yi na hana masu kishin islam shiga harkokin siyasar kasar domin dadadwa kasashen yammacin turai musamman ma haramtacciyar kasar Isra’ila da take da kyakkayawar alaka da kasar a cikin lokutan nan.
Kasar Azarbaijan dai ta taka gagarumar rawa wajen baiwa haramtacciyar kasar damar shiga cikin harkokin musulmi yankin kafkaz, wanda hakan ke nuni da cewa akwai boyayyaen shiri na yin amfani da wannan kasa ta musulmi domin aiwatar da wasu munanan manufofi na kasashe makiya kan musulmi musamman kan jamhuriyar muslunci.
Yanzu haka g wamnatin kasar Azarbaijan ta kafa dokar hana kafa jam’iyya mai taken addini a yunkurin da gwamnatin kasar take yi na hana masu kishin islam shiga harkokin siyasar kasar domin dadadwa kasashen yammacin turai musamman ma haramtacciyar kasar Isra’ila da take da kyakkayawar alaka da kasar da ke cikin kasashen musulmi.
983710