IQNA

Isra’ila Ta Wayi Gari Abun Kyama A Cikin Dukkanin Al’ummomin Duniya

23:59 - April 12, 2012
Lambar Labari: 2303409
Bangaren kasa da kasa, saboda mummunar siyasar haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummar palastine da ma sauran al’ummomin musulmi da na larabawa hakan ya santa ta zama abun ki a duniya fiye da kowane lokaci da ya gabata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na The Ireland Alliance cewa, fiotaccen marubucin nan na kasar Birtaniya David Morrison ya bayyana cewa, saboda mummunar siyasar haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummar palastine da ma sauran al’ummomin musulmi da na larabawa hakan ya santa ta zama abun ki a duniya fiye da kowane lokaci da ya gabata a cikin tarihinta.
Ya ci gaba da cewa al’ummomin duniya suna kara samun wayewa da fadaka kan abubuwan da suke faruwa, wanda kuma hakan shi ne babban dalin mayar da haramtacciyar kasar yahudawan saniyar ware a cikin lamurran al’ummomin duniya, domin kuwa ahalin yanzu ab musulmi ko larabawa ne kawai suke kyamar Isar’ila, har mada turawa da yahudawa da suke bin tafarki da bai yarda da sahyuniyanci ba.
Ya kara da cewa saboda mummunar siyasar haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummar palastine da ma sauran al’ummomin musulmi da na larabawa da sauran al’ummaomin duniya, hakan ya santa ta zama abun ki a duniya fiye da kowane lokaci da ya gabata a cikin tarihin duniya.
983544


captcha