Bangaren kasa da kasa, daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su da ma kisa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine Info cewa, daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.
Daruruwan matasan sun taru ne a wani babban dandali da ke tsakiyar birnin Moscow na kasar Rasha inda suka daga tutoci na kasashen Rasha da kuma palastinedomin nuna cikakken goyon bayansu ga wannan al’umma da take fuskantar zalunci daga yahudawan sahyuniya, tare da amincewa manyan kasashe na duniya kama su Amurka da Birtaniya gami da Faransa da sauransu.
Daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su da yin kisan gilla a kansu.
986270