IQNA

17:33 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309307

Hizbullahi ta Yi Allah Wadai Da Halun Rashin Mutunci Na Sojin Amerika A Afganistan

Bangaren kasa da kasa: bangaren soja na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wata takarda da ta kumshi bayanin yin Allah wadai da halin rashin mutunci da tausayi da kuma ya saba hankalin mutum da sojojin Amerika da ke gudanar da ayyukan mamaye a Afganistan ke yin a takurawa da kisan mummuke kan fararen hula a wannan kasa.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: bangaren soja na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wata takarda da ta kumshi bayanin yin Allah wadai da halin rashin mutunci da tausayi da kuma ya saba hankalin mutum da sojojin Amerika da ke gudanar da ayyukan mamaye a Afganistan ke yin a takurawa da kisan mummuke kan fararen hula a wannan kasa.Majiyar gidan talbijin na Almanar ne ya watsa labarain cewa; hotunan da wata jarida ta Amerika ta nuna na yadda wasu sojojin mamayen Amerika a kasar Afganistan suke yin a cin mutuncin gawarwakin fararen hula bayan sun kasha su kuma yadda suke cin mutunci da kaskantar da gawarwakin mutanan afganistan wani hali ne na takalar fada da neman tada hankalin jama'a da tada zaune tsaye kuma kamar yadda sojojin mamaye na Amerika da gwamnatin Amerike takurawa da cin mutuncin fararen hula da ransu sai gashi wannan dabi'a ta su mummuna ta tashi daga kan aiki hatta gawarwaki ba a barsu a baya ba.
989524
captcha