Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na shoruk news cewa, an fara gudanar da zaman kara wa juna sani kan ilmi da mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi babban dakin taruka na jami’ar Junubul Wadi da ke gundumar Kana a kasar Masar kamar dai yadda kakakincibiyar kula da ayyukan kur’ani ta kasar ya sanar.
Taron dai zai samu halartar masana da malaman kur’ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasar da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi da suke da sha’awar bunkasa harkokin harkokin kure’ani, kamar yadda wasu daga cikin masu nazari a wannan bangaren daga jami’ar Azhar za su halraci taron domin gabatar da maklaolinsu.
Bayanin ya ce an fara gudanar da zaman kara wa juna sani kan ilmi da mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi babban dakin taruka na jami’ar Junubul Wadi da ke gundumar Kana a kasar mai tsohon tarihi ta fuskacin addini da karatun kur’ani.
989657