IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Yaba Da Ci Gaban Da Iraki Ta Samu

19:13 - April 24, 2012
Lambar Labari: 2311978
Bangaren siyasa da zamantakewa, Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagoran juyin juya cewa, Kasar Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran. Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar. Ayatullah Ali Khamenei, ya kara da cewa, Wasu bangarori sun yi ta kokarin nuna cewa kasar Iraki, ba ta da wani matsayi a cikin kasashen larabawa, amma bayan taron kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudana a Bagdada, kasar Iraki, a yanzu na kan gaba a cikin wannan kungiyar, kuma praministan kasar ke jagorantar ta.
A daya waje jagoran, ya bayyana cewa samun nasarori da ci gaban da kasar Iraki za ata yi don tabbatar da matsayinta tsakanin kasashe na iya fuskanatar wasu yan matsaloli, wanda ko dole ne kafin duk wata kasa ta samun yancin kanta da ci gaba da tabbatar da matsayinta tana bukatar shiri na gari da halin da zai sa ta cimma guri wanda mafi mahimmanci daga ciki sune ci gaban kimiya, da sake gina kasar hade da kayutata hanyoyin biya ma jama'ar kasar bukatocinsu, a game da hakan jagoran ya bada misali da kasar Iran, musamman a kan ci gaban kimiya da kasar ta samu da ma wasu sauren ci gaban da ma ba a taba tsamanin samunsu ba. Al halin kasar Iraki ce tushen masanan kimiyan kasashen larabawa, don haka yake ganin ya dace da a samu wani yunkuri na masanan kimiya da zai hada daukacin masana da futattun mutane wanda za su iya samar ma jama'ar kasar ta Iraki kyakyawar rayuwa.
Praminitan kasar ta Iraki, Nuri Al-Maliki, ya nuna jin dadinsa sosai da suka gana da jagoran, inda ya tabbatar da cewa da yardar Allah, hulda tsakanin kasashen biyu za ta dore a kan fannoni da dama, inda tuni dama bangarorin yan kasuwa da kamfanoni ke zarya tsakanin kasashen biyu.
992209

captcha