IQNA

Za A Fitar da Wani Fin Da ke Bayani Kan rayuwar Tsahon Sakataren Hizbullah

17:50 - April 25, 2012
Lambar Labari: 2312240
Bangaren kasa da kasa da kasa, ana shirin fitar da wani sabon fim da ke bayani kan rayuwar tsohon sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah da kuma abubuwan da ya gabatar domin tabbatar da gwqagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ila.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin fitar da wani sabon fim da ke bayani kan rayuwar tsohon sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah da kuma abubuwan da ya gabatar domin tabbatar da gwqagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasar Lebanon da kuma yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Wannan fim din zai tabo bangarori daban-daban na rayuwarsa da suka hada tun daga rayuwarsa ta kuruciya, da kuma yadda ya kasance cikin daliban hauza masu matukar kokari wajen neman ilimi da mayar da hankali ga tarbiyar ruhi, kamar yadda fim din zai yi bayyana wani daga cikin rayuwarsa ta gwagwarmaya tun bayan kafa kungiyar mahrumin kasar Lebanon kafin bayyanar Amal da hizbullah.

Ana shirin fitar da wani sabon fim da ke bayani kan rayuwar tsohon sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah da kuma abubuwan da ya gabatar domin tabbatar da gwqagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasar Lebanon.

Abbas Musawi ya yi shada ne a lokacin da ya gabatar da jawabi a ranar shahadar daya daga cikin jagororin kungiyar ta hizbullah a kudancin kasar Lebanon Sheikh Ragib harba, wanda shi ma ya kasance a sahun gaba wajen yaki da haramtacciyar kasar yahudawan.

993246
captcha