IQNA

Wani Malamin Jami'ar Gwamnatin Tajikistan Ya Keta Alfarmar Kur'ani

17:40 - April 29, 2012
Lambar Labari: 2314511
Bangaren siyasa da zamantakewa, wani malamin jami'a a kasar Tajikistan mai suna Zafar Mirzayan ya yi wani jawabi a gaban talibansa inda ya soke ayoyin kur'ani mai tsarki lamarin da ya bakanta ran dukaknin musulmin kasar baki daya tare da yin kira da a dauki mataki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na amr News, wani malamin jami'a a kasar Tajikistan mai suna Zafar Mirzayan ya yi wani jawabi a gaban talibansa inda ya soke ayoyin kur'ani mai tsarki lamarin da ya bakanta ran dukaknin musulmin kasar baki daya tare da yin kira da a dauki mataki a kansa ta yadda za a kawo karshen duk wani yunkurin irin wannan kasar.
Shugaban majalisar wucin gadi mai mulkin kasar Libya ya musanta labarin cewa majalisar ta kori gwamnatin kasar watannin biyu kacal kafin a gudanar da zabe na farko a kasar.
Mustafa Abduljalil ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters a jiya jumma'a cewa, majalisar wucin gadin bata kori gwamnatin Priminista Abdurrahim Al-Keib ba kuma bata da niyyar yin haka nan kusa.
A ranar Al-Hamis da ta gabata ce wasu kafafen yada labarai suka nakalto Fathi Baja, wani dan majalisar wucin gidan ya na cewa majalisar ta yanke shawarar yin watsi da gwamnatin Al-Keib amma ta boye labarin zuwa wani lokaci. Sai daga baya Fathi Baja ya fito ya musanta wannan labarin.
Kafin haka dai wani mai magana da yawon majalisar ya bayyana cewa majalisar tana binciken ayyukan wasu ministocin a gwamnatin Al-Keib, kuma mai yuwa ta dauki matakan korarsu daga aiki nan gaba.
Mustafa Abduljalil ya tabbatar da cewa wasu yan majalisar wucin gadin sun sami amincewar wasu tokwarorinsu kan sauya gwamnatin kasar amma har yanzun majalisar bata zauna don tattauna batun ba.
994743

captcha