IQNA

Kungiyar Hizbullah Na Da cikakken Shirin Fuskantar Duk Wani Makiyi

20:10 - May 01, 2012
Lambar Labari: 2316349
Bangaren kasa da kasa, mataikin shugaban kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa a halin yanzu kungiyar tana da cikaken shiri na fuskantar duk wani shishigi daga makiya ba tare da wani shayi ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, Sheikh Na’im Kasim mataikin shugaban kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa a halin yanzu kungiyar tana da cikaken shiri na fuskantar duk wani shishigi daga makiya ba tare da wani shayi ba tare da kore duk wani jijita jita kan bayar da taimako ga gwamnatin Syria domin murkushe ‘yan ta’adda.
Al’ummar kasar Syria sun fiito kanmamnyan titinan ksar domin nuna rashin amincewarsu da shigar shigular da wasu kasashen suke yi a cikin harkokin kasar da nufin wargaza duk wani shirin zaman lafiya da tsohon sakataren majalisar dinkin duniya ke jagoranta.
A bangare guda kuma wani bayanin ya ce gwamnatin Syria ta aike da wasu wasiku biyu zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya da kuma shugaban kwamitin tsaron majalisar, dangane da karuwar ayyukan ta'addanci bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
A cikin wasikun biyu, gwamnatin Syria ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta safke nauyin da ya rataya a kanta, wajen matsa lamba kan gwamnatocin da suke taimaka ma ayyukan ta'addanci a cikin kasar Syria, ta hanyar baiwa 'yan bindiga makamai da makudan kudade, domin kuwa a cewar bayanin, idan har gwamnatin Syria za ta amince da wannan yarjejeniya da kuma yin aiki da ita, babu dalilin da zai sanya a bar daya bangaren rikicin yana cin karensa babu babbaka.
Bayanin ya ce tawagogi na masu sanya ido na kasashen larabnawa da majalisar dinkin duniya sun gane wa idanunsu hakikanin abin da ke faruwa a kasar, saboda haka kawo karshen tashin hankali a kasar ya doru ne kan dakatar da kasashen masu taimaka ma ayyukan ta'addanci, musamman ma na larabawa daga cikinsu, wadanda suka sanar da hakan a hukumance. 996415
captcha