IQNA

Abin Da 'Yan tawayen Syria Ke Yi Ya Hannun Riga Da Boren Kasashen Larabawa

13:33 - May 06, 2012
Lambar Labari: 2319457
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masana suna cewa, abin da 'yan tawayen kasar Syria n ayyukan ta'addanci ya yi hannun riga da abin da ake yi a cikin wasu kasashen larabawa na neman 'yanci daga shugabanninsu 'yan kama karya dab a su gudanar da guyare-gyare na neman 'yanci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu daga cikin masana suna cewa, abin da 'yan tawayen kasar Syria n ayyukan ta'addanci ya yi hannun riga da abin da ake yi a cikin wasu kasashen larabawa na neman 'yanci daga shugabanninsu 'yan kama karya dab a su gudanar da guyare-gyare na neman 'yanci, domin kuwa abin da suke yi ta'dddanci ne.
Jami'an tsaron kasar Syria da ke gadin kan iyakokin kasar sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga da suka yi nufin shigowa cikin kasar daga kasar Turkiya dauke da makamai, lamarin da ya tilsta 'yan bindigar komawa cikin kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, gungun 'yan ta'addan sun sadado ne a kan iyakar kasar Syria da Turkiya a kusa da garin Idlib, amma dakarun gwamnatin Syria sun yi musu kwantan bauna, lamarin da ya kai ga musayar wuta a tsakaninsu, rahoton ya ce wasu daga cikin 'yan ta'addan sun rasa rayukans wasu kuma sun samu raunuka.
A jiya ne dai wasu bama-bamai da ake zaton cewa 'yan ta'addan na kasar Syria suka dasa su suka tarwatse a birane biyu mafi girma na kasar, wato Damascus da kuma Aleppo, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da jami'an tsaro, tare da jikkatar wasu. 1000168
captcha