Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban dakarun sa kai na kasar Iran ya sheda cewa irin matakan dabbanci da rashin 'yan adamtaka da wasu daga cikin mutanen kasashen yammacin turai suke dauka na kone kur'ani mai tsarki babbar alama ce da ke tabbatar da gazawarsu kan wannan littafi mai tsarki wanda ke shiryar dad an adam zuwa ga ubangijinsa kuma shi rahma ne ga dukaknin talikai na duniya baki daya.
A dai dai karfe 8 na safiyar yau Jumma'a ce aka fara zaben yan majalisar shawarar musulunci zagaye na biyu a mazabu 14,323 a cikin yankuna 33 a duk fadin kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar ta Iran ya bayyana cewa, yan takara 130 ne suke takarar cike kujeru 65 da suka rage a majalisar shawarar ta musulunci.
An gudanar da zagaye na farko na zaben majalisar shawarar musulunic a ranar 12-Esfan-1390 H.SH. Jumma'am 02-Maris-2012M.
Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Ali Khaminaee ya kada kuri'arsa a cikin akwati mai lamba 110, sannan ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri'arsu a zabe na yau da su fito kamar yadda suka fito a zagaye na farko don zuben wakilan da suka cancanta a wannan karon ma.
999923