IQNA

22:01 - May 09, 2012
Lambar Labari: 2322515

Kimanin Italiyawa Dubu 70 Ne Suka Musulunta A kasar A Lokutan Da Suka Gabata

Bangaren kasa da kasa, gamayyar kungiyoyin musulmi na kasar Italitya ta bayyana cewa kimanin turawan italiya dubi saba’in da suka musulunta suka yi rijistar sunayensu a wanna cibiya kuma suke da kyakyawar dangantaka da ita tare da sauran musulmi da suke kasar wadanda suka zo daga wasu kasashe.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, gamayyar kungiyoyin musulmi na kasar Italitya ta bayyana cewa kimanin turawan italiya dubi saba’in da suka musulunta suka yi rijistar sunayensu a wanna cibiya kuma suke da kyakyawar dangantaka da ita tare da sauran musulmi da suke kasar wadanda suka zo daga wasu kasashe musamman ma na larabawa da musulmi.
A wani labari kuma masu kare hakkokin dan adam dag akasashen duniya suna ci gaba da yin kakakusar suka kan gwamnatin wahabiyanci ta Saudiyya da ta daina cin zarafin dan adam tare da keta hurumin akidun sauranm muuslmi da suke zaune a kasar da suka daba wa akidar wahabiyanci da gwamnatin kasar ta ginu a kanta, musamman ma dai mabiya tafarkin manzon Allah da iyalan gidansa.
Da dama daga cikin malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa kan fararen hula.
1003091




captcha