Bangaren kasa da kasa, babban daraktan cibiyar Nusratul kur’ani da ke da babban ofishinta akasar Iraki wadda kan dauki nauyin shirya gasar kur’ani mai tsarki ta kasa ya kawo ziyara a ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na Iqna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Mazin Sa’idi babban daraktan cibiyar Nusratul kur’ani da ke da babban ofishinta akasar Iraki wadda kan dauki nauyin shirya gasar kur’ani mai tsarki ta kasa ya kawo ziyara a ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na Iqna da ke birnin Tehran, domin ganewa idanunsa irin ayyukan da wannan kamfanin dillancin labarai yake gudanarwa.
Malamin ya gana da manyan jami’ai na kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna, inda ya yaba da irin ayyukan da suke gudanarwa na bayar da labarai da suka shafi kur’ani mai tsarki daga dukkanin sassa na duniya, kamar yadda labaransa ba su takaita da na kur’ani ba, har labarai da suka dangaci siyasar duniyar musulmi duk yana mayar da hankali kanta, domin muuslmi su zama cikin fada da sanin abin da lke gudana a duniyarsu.
Sheikh Sa’idi babban daraktan cibiyar Nusratul kur’ani da ke da babban ofishinta akasar Iraki wadda kan dauki nauyin shirya gasar kur’ani mai tsarki ta kasa ya kawo ziyara a ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na Iqna da ke Iran.
1005844