Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da lokacin gudanar da zaben kasar Masar ya rage kasa da makonni biyu masu zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ta fito karara ta nuna matukar damuwarta dangane da makomar alaka tsakaninta da kasar Masar bisa la’akari da cewa duk wanda ya samu nasara a cikin wadanda suke kan gaba da wuya ya shirya da ita.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-akhabar ta kasar Lebanon cewa, a daidai lokacin da lokacin gudanar da zaben kasar Masar ya rage kasa da makonni biyu masu zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ta fito karara ta nuna matukar damuwarta dangane da makomar alaka tsakaninta da kasar Masar bisa la’akari da cewa duk wanda ya samu nasara a cikin wadanda suke kan gaba da wuya ya shirya da ita musamman idan aka yi la’akari da kalaman da suka furta a lokutan baya kan hakan.
Dangantaka tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ial da masar dai ta rauni tun bayan kawar da babban aminta a kasar wato Husni Mubarak wanda ya kasance shugaban mulkin kama karya tare da kare manufofin yahudawan sahyuniya ayankin gabas ta tsakiya, kuma kawar da al’ummar Masar suka yi ya zama wata babbar alama ta kawo karshen kyakyawar alaka tsakanin kasar Masar da hara,mtacciyar kasar yahudawan.
Lokacin gudanar da zaben kasar Masar ya rage kasa da makonni biyu masu zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ta fito karara ta nuna matukar damuwarta dangane da makomar alaka tsakaninta da kasar Masar bisa la’akari da cewa duk wanda ya samu nasara a cikin wadanda suke kan gaba da wuya ya shirya da ita a bayan samun nasara.
1006987