Bangaren kasa da kasa, shugaban jam’iyyar masu kishin islama da ke da tsatsauran ra’ayi a kasar Algeria ya bayyana cewa za a iya samun canji irin wanda suke bukata a mahangarsa a kasar ne ta hanyar juyin juya hali kawai ba ta hanyoyi na siyasa da zaman lafiya ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lofigaro cewa, Abdullahi Jablah shugaban jam’iyyar masu kishin islama da ke da tsatsauran ra’ayi a kasar Algeria ya bayyana cewa za a iya samun canji irin wanda suke bukata a mahangarsa a kasar ne ta hanyar juyin juya hali kawai ba ta hanyoyi na siyasa da zaman lafiya ba da lumana ba.
Ya furta hakan ne a lokacin da yake sukar gwamnatin kasar tare da zargin cewa ta tafka magudi a zabukan da aka gudanar a kasar na ‘yan majalisar dokoki, hakan kuwa ya biyo bayan kayin da jam’iyyarsa ta sha ne, duk kuwa da kawancen da ta yi tare da wasu daga cikin masu kishin islama amma ba samu damar zuwa ko da mataki na biyu ba ne, duk kuwa da cewa kafin lokacin sun sun sakankance kan cewa su ne za su kwace mulki daha jam’iyya mai mulki.
Abdullah Jablashugaban jam’iyyar masu kishin islama da ke da tsatsauran ra’ayi a kasar Algeria ya bayyana cewa za a iya samun canji irin wanda suke bukata a mahangarsa a kasar ne ta hanyar juyin juya hali kawai ba ta hanyoyi na siyasa ba, duk kuwa da cewa al’ummar kasar sun san da abin da ke faruwa akasashen larabawa amma suka zabi su sauna lafiya. 1007458