IQNA

Yan Majalisar Iran Sun Yi Kakkausar Suka Kan Yunkurin Saudiyya Na Mallake Bahrain

21:19 - May 15, 2012
Lambar Labari: 2326801
Bangaren siyasa, wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin jamhuriyar musulunci ta Iran sun yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da matakin da masarautar kasar Saudiyya ta dauka na mallake kasar Bahrain ba tare da amincewar mutanen kasar ba a wani mataki na tabbatar da ikonta kan sauran kasashen yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kimanin mutane 190 yan majalisar dokokin jamhuriyar musulunci ta Iran sun yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da matakin da masarautar kasar Saudiyya ta dauka na mallake kasar Bahrain ba tare da amincewar mutanen kasar ba a wani mataki na tabbatar da ikonta kan sauran kasashen yankin musamman kan kanan kasashen larabaw ada suke yankin.
Masana da masu bin diddigin abin da ke faruwa a yankin sun yi imanin cewa masarautar kasar Bahrain karakshin mulkin gidan khalifa suna yin abin da haramtatcciyar kasar Isra’ila ma ba ta yi na tsabar zalunci da danne hakkkokin mutanen kasar marassa kariya kamar yadda kuma sauran kasashen dunbiya suke ba ta kariya kan wannan ta’addanci kan fararen hula.
Sheikh Isa Kasim babban malamin addinin muslunci kuma limamin kasar Bahrain ya bayyana cewa mahukuntan kasar manyan makaryatane domin kuwa suna bayyana ma duniya wani abu daban sabanin abin da suke aikatawa na ta’addanci da zalunci kan al’ummar kasar marassa kriya.
1007783


captcha