IQNA

21:21 - May 16, 2012
Lambar Labari: 2327689

Za A Gudanar Da Zaman Taro Kan fadakar Musulmi A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Bangaren siyasa da zamantakewa, ana shirin gudanar da zaman taro kan fadakar al'ummar musulmi da larabawa a yankin gabas ta tsakiya da kuma tasirin haka a cikin sauran kasashe da ma ban a musulmi ba kamar yankunan nahiyar turai da sauransu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin gudanar da zaman taro kan fadakar al'ummar musulmi da larabawa a yankin gabas ta tsakiya da kuma tasirin haka a cikin sauran kasashe da ma ban a musulmi ba kamar yankunan nahiyar turai da sauransu da haka ya hada hard a Amurka.
Majalisar shawarar Musulunci ta Iran ta yi Allawadai da kokarin da kasar saudia da Amurka suke yi na hade kasar Bahrai da ita saudia, a cikin wata sanarwa wacce yan majalisar 190 suka sanyawa hannun, majalisar ta bayyana a jiya litinin cewa, nuna karfi ba zai taba warware matsalar kasar Bahrain ba. Kuma matakin hade ita Bahrain da saudia zai kara yada rikicin ne kawai.
Tun ranar 14-Maris na shekarar bara ne dai sojojin kasar Saudia 1000 guda suka shiga kasar Bahrain don tallafawa jami'an tsaron kasar murkushe borin da mutanen kasar suke wa sarakunan kasar.
Kasar Saudia dai ta bayyana anniyarta na dunkulewarta da sauran kasashen larabawa na yankin tekun Parisa 5, wato Bahrai, Kuwait, Qatar, Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Oman, don fuskantar abinda ta kira barazanar da suke fuskanta.
A jiya ne kasashen 6 suka gudanar da zamansu na farko a kan wannan manufar amma sun tashi ba tare da sun cimma wani abin a zo a gani ba kamar dai yadda suka saba yi.
1008832

captcha