IQNA

Jagororin Addinai Na Da rawar Da Za Su Taka Wajen Kusanto Da Fahimtar Mutane

21:47 - May 17, 2012
Lambar Labari: 2328090
Bangaren kasa da kasa, jagororin addini suna da gagarumar rawar da za su iya takawa ta fuskacin hada kan mabiyansu da kuma kusanto da fahimtar mutane ta yadda hakan zai bayar da damar samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin mabiya addinai na duniya musamman ma wadanda aka safkar daga sama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya sheda cewa, a wata zantawa da tta hada shi shugaban majali’ar Arthodocs a kasar Girka ya sheda cewa jagororin addini suna da gagarumar rawar da za su iya takawa ta fuskacin hada kan mabiyansu da kuma kusanto da fahimtar mutane ta yadda hakan zai bayar da damar samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin mabiya addinai na duniya musamman ma wadanda aka safkar daga sama da suka hada da musulunci da kiristanci da kuma yahudanci.
Ya ce kasa da makonni 3 da keta alfarmar kur'ani mai tsarki ta hanyar kone shi da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afghanistan, sojin na Amurka sun sake tafka wata ta'asar da ta kara fito da dabi'arsu ga al'ummar kasar Afghanistan da sauran al'ummomin duniya baki daya, inda daya daga cikinsu ya yi kisan gilla a kan fararen hula 18 a lokacin da suke barci a cikin gundimar Kandahar a Lahadin da ta gabata.
Mutanen kauyen Panjwai da ke cikin gundumar Kandar da ke kudancin kasar Afghanistan sun sheda cewa, sojan na Amurka ya biyo dare ne, a lokacin da ya balle kofofin gidaje uku a kauyen a lokacin da mutane suke barci, inda ya bude wuta kansu, a nan take ya kashe fararen hula 17 da suka hada da mata da kananan yara, ya kuma jikkata wasu da dama.
Wannan mummunan aikin ta'addanci ya jawo fushin al'ummomin kasar ta afganistan da ma sauran kasashen duniya, inda har yanzu ake ci gaba da yin Allawadai da gwamnatin Amurka da kuma ayyukanta na ta'addanci kan fararen hula a kasar Afghanistan.
A wani mataki na borin kunya, bayan da dukkanin al'umomin duniya suka samu bayanin abin da ya faru, rundunar tsaro ta NATO ta yi kokarin nisanta kanta da wannan danyen aiki, tare da dora alhakin hakan kan sojan na Amurka, yayin da shi kuma shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya sheda wa shugaban kasar Afghanistan cewa za gudanar da bincike kan lamarin, duk kuwa da cewa har yanzu ba a san dalilin da ya sanya sojan na Amurka yin wannan kisan gilla kan wadannan fararen hula ba, amma shugaban kasar ta Afghanistan ya yi Allawadai da hakan, tare da bayyana cewa wannan mummunan aiki ba abu ne da al'ummar Afghanistan za su yafe shi ba. 1002005
captcha