IQNA

Daliban Jami’a A Pakistan Sun Bukaci Nuna goyon Baya Ga Al’ummar Palastinu

20:52 - May 19, 2012
Lambar Labari: 2329323
Bangaren siyasa da zamantakewa, daliban jami’a mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Pakistan sun bukaci da a nuna cikakken goyon baya ga al’ummar apalstinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya tare da hadin baki da wasu daga cikin munafukan larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa daliban jami’a mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Pakistan sun bukaci da a nuna cikakken goyon baya ga al’ummar apalstinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya tare da hadin baki da wasu daga cikin munafukan larabawa da suke yankin gabas ta tsakiya.
Al’ummar palastinu jigo ne mai matukar muhimmanci a cikin dukaknin lamurra da suka danganci fadakar da al’ummar musulmi ta yi a wannan zamani musamman ma ganin cewa ita al’umma ce da ta farka tun shekaru da dama da suka gabata tana gwagwarmayar neman ‘yancinta da hakkokinta daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
A nata bangaren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka.
1008961


captcha