Bangaren kasa da kasa; fatawar da ayatullahi Al'uzma Khamna'I ya fitar ta haramta amfani da makamin nukliya a matsayinsa na makamin kare dangi` a gaskiya wannan na nuni da gaskiyar jamhuriyar musulunci ta Iran na cewa shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya da sulhu ne sabanin farfaganda da ake yadawa cewa tana kokarin mallakar makaman nukliya ne.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: fatawar da ayatullahi Al'uzma Khamna'I ya fitar ta haramta amfani da makamin nukliya a matsayinsa na makamin kare dangi` a gaskiya wannan na nuni da gaskiyar jamhuriyar musulunci ta Iran na cewa shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya da sulhu ne sabanin farfaganda da ake yadawa cewa tana kokarin mallakar makaman nukliya ne.Narjes bin Abada wata fitattciyar mai sharhi kuma mamba a komitin fada da yahudawan sahayoniya na Colectif Chalon Palestine a Faransa a wata tattaunawa da ta hada tad a kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; jagoran juyin juya halin musulunci na Iran kuma daya daga cikin fitattun maraji'ai da jagororin yan shi'a ba ma kawai a Iran ba a duniya ma bakiya ya fitar da fatawar haramta mallakar makamin nukliya na kisan kare dangi kan jama'a to hakan ko shakka babbu yana nufin gaskiyar jamhuriyar musulunci ta Iran kan shirinta na nukliya cewa na zaman lafiya ne.
1011011