Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar yaum sabi cewa, Mujtaba Amani babban jami’i mai kula da ayyukan jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar Masar a lokacin da yake zantawa da babban malamin jami’ar Azhar ya bayyana cewa akwai wasu wadanda babban burinsu shi ne su ga sun haifar da matsaloli da rikici tsakanin mabiya tafarkin muslunci da sunan banbancin mazhaba a tsakaninsu domin yin hidima ga makiya muslunci.
A wani labarin kuma an buga tare da wani littafi da aka dangata shi da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da nufin kawo baraka da rarraba kawunan mabiya addinin muslunci a kasar Indonesia wanda makiya musulunci tare da munafukai daga cikin musulmi masu yi makiya aiki ne suka shirya hakan domin cimma boyayyar manufarsu kan addinin muslunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi ya kunshi kalamai na batunci ga wasu daga cikin sahabban manzon Allah da wasu daga cikin matansa, wanda hakan ba zai yi dukaknin musulmi shi da sunna dadi ba, amma kuma a lokaci guda wadanda suka rubuta wannan littafi tare da bugfa shi da yada shi suna kokarin danganta dukkan wannan aiki da suka yi na bata sahabban manzo da matansa ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.
An buga tare da wannan littafi ne da aka dangata shi da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da nufin kawo baraka da rarraba kawunan mabiya addinin muslunci a kasar Indonesia wanda makiya musulunci tare da munafukai daga cikin musulmi masu yi makiya aiki ne suka shirya hakan kamar yadda suka saba yia tsawon zamunan baya.
1013766