IQNA

13:59 - May 26, 2012
Lambar Labari: 2334252

Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Masar Zagaye Na Biyu Tsakanin Marsi Da Shafiq

Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaben shugfaban kasar Masar zagaye na biyu tsakanin ‘yantakara biyu na kungiyar Ikhwanul muslimin da kuma Muhammad marsi da kuma mai zaman kansa kuma tsohon pira minista alokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak Ahmad Shafiq.

Kamfanin dilalnbcin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, ana shirin gudanar da zaben shugfaban kasar Masar zagaye na biyu tsakanin ‘yantakara biyu na kungiyar Ikhwanul muslimin da kuma Muhammad marsi da kuma mai zaman kansa kuma tsohon pira minista alokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak Ahmad Shafiq wadanda dukakninsu suka samu kuri’u fiye da na sauran a zagayen farko.
Masu zabe sun fito a rana ta biyu don zaben shugaban kasa a kasar Masar a yau Alhamis. Duk da cewa wasu suna ganin fitowar masu zaben shugaban kasa a jiya laraba bai kai na zaben yan majalisar dokokin kasar ba. Amma duk da haka fitowar tana da yawa har sai da wasu suka kasa kada kuri'arsu a jiya don yawan masu zabe, don haka ne suka fito a yau don kada kuri'arsu.
Babu wanin tashin hankali da ya faru a zaben a jiya dai, inda banda duwatsu da takalma da aka jefa kan dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon Priminister a lokacin Mubarak wato Ahmad Shafiq, a lokacin da ya je rumfan zabe don kada kuri'arsa.
Kungiyar Ikhwanul muslimin dai ta bada sanarwan cewa dan takararta Muhammad Mursi, shi ne a gaba, hakama masu goyon bayan Amru Musa sun bayyan cewa dan takarar ikhwanul muslimin ne a gaba sannan dan takaransu Amru Musa yana biye da shi.
Idan babu dantakaran da ya sami fiye da kashi 50% daga cikin kuri'in da aka kada dai to sai an je zagaye na biyu a ranakun 16 da 17 na watan yuli mai zuwa tsakanin yan takararn da suka fi samun kuria guda biyu.
1016184
captcha