IQNA

An Bukaci Yanke Hukunci Kisa Kan Tsohon Shugaban Mulkin Kama Karya Na Tunisia

13:58 - May 26, 2012
Lambar Labari: 2334254
Bangaren kasa da kasa, an bukaci yanke hukuncin kisa kan tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Tunisia Zainul Abidin wanda yanzu haka gwamnatin wahabiyan saudiyya take ba shi mafakar siyasa a cikin kasar duk kuwa da irin barnar da ya tafka kan al’ummar kasar a lokacin da yana kan karagar mulki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio na tashar jazira cewa, an bukaci yanke hukuncin kisa kan tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Tunisia Zainul Abidin wanda yanzu haka gwamnatin wahabiyan saudiyya take ba shi mafakar siyasa a cikin kasar duk kuwa da irin barnar da ya tafka kan al’ummar kasar a lokacin da yana kan karagar mulki wanda ya kasance yana dasawa da Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila da sauran kasashen turai.
Wani mai gabatar da kara a wata kotu a kasar Tunisia yan bukaci kotu ta yanke hukunci mafi tsakani wato kisa kan tsohon shugaban kasar Zainul Abideena bin Ali wanda a halin yanzu yake gudun hijira a kasar Saudia, kamfanin dillancin labarai na TAP na kasar Tunisia ya bayyana cewa, mai gabatar da kara a garin Kef na kudancin kasar har'ila yau ya bukaci a yanke hukuncin kisa kan duk wanda yake da hannu kan kisan masu zanga zanga a lokacin borin da ya kifar da gwamnatin Zainul Abedeen a karshen shekara ta 2010.
Tuni dai wasu kotuna a kasar ta Tunisia sun yanke hukuncin zaman gidan yari na shekaru masu yawa ga tsohon shugaban kimanin masu zanga zanga 300 ne dai suka rasa rayukansu a borin na shekarar bara, kuma a halin yanzu wasu iyalan wadanda aka kashen, suna zargin gwamnatin kasar a halin yanzu da yin sako sako wajen takurawa kasar saudia ta mika tsohon shugaban kasar don ya fuskanci adalci.
Banda wannan ya zuwa yanzu yansanda 2 ne kacal aka hukunta da laifin kashe masu zanga zanga a lokacin borin. Babu wani babban jami'in tsohuwar gwamnatin da ya gurfana a gaban kotu kan kisan masu bori.
1016126
captcha